Ma'aikatan bankuna a Nijar sun shiga yajin aiki
May 20, 2013Kungiyar ma'aikatan bankunan a Jamhuriya Nijar sun shiga yajin aikin kwanaki biyu, domin cilastawa gwamnatin kasar,ta rage yawan haraji da ta take cirewa cikin albashin ma'aikatan.
A yayin da yake baiyani da kamfanin dullancin labaran AFP, Sakatare Janar na kungiyar ma'aikatan bankunan Nijar Lawali Hima, ya ce a shekara 2012 sun rattaba hannu kan yarejejeniya da gwamnati, wadda ta yi tanadin ragin kashin 20 cikin dari na harajin da ake cirrwa ga albashinsu, to amma har ya zuwa wanan lokaci ya ce gwamnati ba ta cika wannan alkawari ba.
A ranar farko yajin aikin ya samu karbuwa a manyan biranen kasar.
A jamhuriya Nijar dake matsayin daya daga kasashen da suka fi talauci a duniya, mutane kalilan ne ke da kudaden ajiya a cikin bankuna.
Yajin aikin na ma' aikatan bankuna ya fara a daidai lokacin da jami'an kiwan lafiya suka dakatar da nasu bori, bayan yarejejeniya da suka cimma tare da gwamnati.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Usman Shehu Usman