M23 ta zargi DRC da yin wasa da tattaunawar zaman lafiya
March 17, 2025Kungiyar M23 mai samun goyon bayan Rwanda ta zargi gwamnatinJamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango da neman yi wa tattaunawar zaman lafiya kafar ungulu.
An dai tsara cewa za a tattauna a kasar Angola tsakanin 'yan tawayen da kuma gwamnatin DRC da ke yakarsu a gabashin kasar bayan kwace iko da wasu manyan birane.
Dalilin tasirin 'yan tawayen M23 a kan sojojin Kwango
Mai magana da yawun M23 da kuma kungiyar Congo River Alliance ya zargi DRC da amfani da jirage maras matuka wajen yin ruwan wuta kan wuraren da ke dankare da jama'a a baya-bayan nan.
Lawrence Kanyuka ya wallafa a shafinsa na X cewa wannan farmakin na Kwango ya nuna aniyarta ta yin zagon kasa ga tattaunawar da aka jima ana neman ganin ta auku.
An nada masu shiga tsakani a rikicin kasar Kwango
Shugaban kasar Angola Joao Lourenco ya bukaci a tsagaita wuta daga ranar Lahadi da dare, to amma babu wanda ya mayar da martani kan kiran nasa tsakanin DRC da M23.