SiyasaAfirka
Nijar: Kwararrun likitoci sun fasa yajin aiki
January 20, 2021Talla
Tun da farko likitocin da sune ke da alhakin kula da masu cutar corona a kasar, sun kuduri shiga yajin aikin na kwanaki uku ne saboda rashin biyansu kudade na albashi da suka kai na watanni bakwai. Sai dai ganawar da shugabannin likitocin suka yi da ministan lafiyar Nijar ta cimma matsayar za a biya su albashin zuwa watan gobe mai kamawa.
Babban Sakatare-Janar na kungiyar likitocin ta SYNPHAMED Dr.Illa Alasan ya shaida wa DW cewa sun ga alamun gwamnati za ta cika alkawarinta shi ya sa suka janye yajin aikin.
Sai dai kuma wakilinmu na Yamai Mamman Kanta ya ce a gefe guda kananan likitoci da ke shiga yankunan karkara sun kuduri aniyar ci gaba da yajin aiki daga wannnan Laraba sakamakon rashin cimma wata matsaya da gwamnatin kasar.