Libiya za ta samu tallafin duniya don sake gina ta
August 31, 2011A yayin da ƙasashen duniya ke hallara domin gudanar da babban taron tattauna batutuwan da suka shafi makomar ƙasar Libiya a birnin Paris na ƙasar Faransa, Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana ƙudirin tallafawa ƙasar domin ta samu damar komawa ga bin tafarkin dimoƙraɗiyya, bayan kawar da Gadhafi daga mulki.
Bayan ɗaukar tsawon watanni shidda ana gwabza yaƙi tsakanin 'yan tawayen Libiya dake samun goyon bayan Dakarun ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO da kuma dakarun dake biyayya ga shugaba Gadhafi daya kai 'yan tawayen ga ƙwace Tripoli, babban birnin ƙasar, kana a yanzu kuma ke shirin tattauna hanyar karɓe iko da birnin Sirte - mahaifar shugaba Gadhafi, Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanar da ƙudirin tallafawa ƙasar ta Libiya domin samar da cibiyoyin tabbatar da tsarin mulkin dimoƙraɗiyya idan aka yi la'akari da cewar kusan babu wani sahihin zaɓen daya gudana a ƙasar da za'a iya cewar ba ta da tsarin dimoƙraɗiyya, kama daga hukumar zaɓe ko tarihin jam'iyun siyasa ya zuwa ƙungiyoyin farar hula masu zaman kansu da dai sauran ginshikan kafofin dimoƙraɗiyya.
A cewar babban mai baiwa sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon shawara akan tsara makomar Libiya bayan kawar da Gadhafi wato Ian Martin ko da shike mai yiwuwa Libiya ba ta buƙatar dakarun ƙetare a cikin ƙasar, amma kuma tana buƙatar tallafi daga ƙetare wajen gina tsarin dimoƙraɗiyya. Ya kuma ƙara da cewar mai yiwuwa majalisar wucin gadin Libiya ta buƙaci Majalisar Ɗinkin Duniya ta taimakawa ƙasar da wata rundunar 'yan sandan da za ta bayar da horo da kuma masu sanya ido akan harkokin ƙasar, wadda Ban Ki Moon ɗin ya ce makamai ya mamaye ta sakamakon yaƙin basasan da aka yi
" Ya ce ba zan iya jaddada muhimmancin ɗaukar matakan gaggawa ba a dai dai wannan lokacin. 'Yan Libiya suna hanƙoron ganin ƙasashen duniya sun taimaka musu, kuma a 'yan kwanakin dake tafe ne gwamnatin wucin gadin Libiya za ta gabatar da buƙatun ta. Burin da na sanya a gaba shi ne hanzarta samar da jami'an Majalisar Ɗinkin Duniya da za su gudanar da aikin."
A halin da ake ciki dai, majalisar wucin gadin Libiyar za ta samar da gwamnati - a hukamance ne cikin tsukin kwanaki 30 bayan nasarar da ta bayyana samu a birnin Tripoli, kana ta shirya zaɓe cikin wa'adin kwanaki 240.
Wannan bayanin yana zuwa ne a dai dai lokacin da wasu manazarta ke cewar, ƙungiyar tarayyar Afirka za ta fuskanci matsala wajen tafiyar da lamuranta na yau da kullum, bisa la'akari da yiwuwar katsewar tallafin da take samu daga gwamnatin Gadhafi, tallafin da kuma wataƙila ba za ta samu ba daga 'yan tawayen dake kan hanyar tafiyar da harkokin ƙasar a yanzu. Farfesa Adams Oloo na jami'ar birnin Nairobi a ƙasar Kenya ya danganta jan-ƙafar da ƙugiyar ke yi wajen amincewa da majalisar wucin gadin 'yan tawayen da wannan dalilin:
" Ya ce Gadhafi ne ya yi ruwa da tsaki wajen samar da ƙungiyar Tarayyar Afirka, kana kuma yake kan gaba wajen bata tallafin kuɗi. Saboda haka, kamar dai sauran shugabannin Afirka, a kullum ƙugiyar tarayyar Afirka za ta kasance a sahun baya, wataƙila a cikin ƙungiyar akwai waɗanda ke zaton yiwuwar sake dawowar sa mulki, kuma ba sa ƙaunar ganin an sanya su cikin jerin masu adawa da Gadhafi."
A can Libiyar kuwa, dubun-dubatan 'yan ƙasar ne suka yi dafifi zuwa dandalin Shahidai dake birnin Tripoli domin halartar Sallar Idi bayan kawo ƙarshen azumin watan Ramadan a safiyar wannan Larabar, inda a huɗubar da ya gabatar limamin da ya jagoranci Sallar ya buƙaci 'yan ƙasar su zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya, bayan kawar da shugaba Gadhafi..
A ƙasa za ku iya sauraron hiran da Usman Shehu Usman ya yi da Hajiya Falmata wata 'yar asalin jahar Borno da ke zama a birnin Tripoli inda ta bayyana halin da suke ciki bayan da 'yan tawaye suka karɓi iko a Libiya. Kana akwai rahoto kan rawar da MMD za ta taka a sake gina Libiya dama irin yadda hulda tsakanin 'yan tawayen libiya da ƙasar Rasha za ta kasance a gaba.
Mawallafi: Saleh Umar Saleh
Edita: Usman Shehu Usman