Lebanon ta gargadi Iran kan yi mata shisshigi
August 13, 2025Shugaban kasar Lebanon Joseph Aoun ya shaida wa sakataren hukumar koli ta tsaron Iran Ali Larijani kin amincewa da duk wani katsalandan ga harkokin kasarsa na cikin gida, bayan da Teheran ta caccaki shirin Bayrout na kwancewa kungiyar Hezbollah damara.
Karin bayani: Gwamnatin Lebanon ta kuduri aniyar kwancewa Hezbollah damara
A cikin watan sanarwa da fadar shugaban Lebanon ta watsa a ranar Laraba a shafin X, ta ce daga yanzu an haranta wa duk wata kungiyar daukar makamai musamman ma tare da tallafin wata kasar waje, sannan kuma tsaron kasar ya rataya a kan gwamnati da kuma halastaciyar rundunar sojoji.
A ranar Asabar da ta gabata ce dai wani mai ba da shawara ga shugaban addinin Iran ya bayyana rashin gamsuwa dangane da matakin gwamnatin Lebanon na kwacewa Hezbollah damara, abin da Bayrout ta bayana a matsayin shisshigi ga harkokinta na cikin gida.