Kwararrun MDD da ke aiki a Gaza da Isra'ila sun yi murabus
July 15, 2025Talla
Murabus din, wanda kwamitin kare hakkin bil'adama mai samun goyon bayan MDD ya sanar, na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tashe tashen hankula a yankunan Falasdinawa, kuma babu alamun ja baya a yakin da sojojin Isra'ila ke yi da kungiyar Hamas da sauran masu gwagwarmaya a Gaza.
Gwamnatin Isra'ila ta sha sukar kwamitin kwararrun na MDD da aka fi sani da kwamitin bincike kan yankin Falasdinu da Isra'ila ta mamaye, tare da musanta bukatar da suke yi na neman shiga yankin ko kuma ba da hadin kai ga tawagar.
Jami'an kiwon lafiya a zirin gaza sun ce hare-haren da Isra'ila ta kai daga daren jiya zuwa wayewar garin yau Talata, sunyi sanadiyyar mutuwar Falasdinawa sama da 90 a Gaza, ciki har da mata da kananan yara da dama.