Kwango na son bai wa Amurka ma'adinai
March 20, 2025Talla
Shugaba Felix Tshisekedi ya fadi hakan ne a wata hira da kafar watsa labarun Fox News da ke a birnin New York, inda ya ce Kwango za ta amince Amurka ta kwashi ma'adinan da kafanoninta za su amfana da su, yayin da ita kuma Kwango za ta samu damar karafafa tsaronta.
Haka nan a cikin kalamansa, Shugaba Tshisekedin ya ce yana ganin Amurka na iya amfani da karfi ko takunkumai da za su taka wa kungiyoyin tawaye burki a kasarsa.
Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da ke da arzikin ma'adinan Cobalt da Lithium da Uranium da ma karin wasu, ta kwashe lokaci tana fama da rikicin 'yan tawaye, inda mayakan kungiyar M23 ke kwace mata yankuna.