Kabila ya isa birnin Goma
May 28, 2025
Bayyanar Joseph Kabila a Goma na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ya zo wa mazauna birnin da mamaki, saboda birnin na hannun 'yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Ruwanda. Sai dai kasancewar tsohon shugaban kasar Kwango a yankin da 'yan tawayen AFC-M23 ke da karfin fada a ji na rage fatan samun warware rikicin gabashin DR Kwango cikin lumana.
Karin Bayani: Me ya hana kawo karshen rikicin Kwango?
Matakin Joseph Kabila na komawa birnin Goma na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango na zuwa ne bayan zarginsa da gwamnatin Kinshasa ta yi na marar hannu wajen tayar da zaune tsaye a gabashin kasar. Sai dai Raphaël Sindani, wani mazaunin babban birnin lardin Kivu ta Arewa ya ce bai kamata hakan zai sauya bala'in da Goma ke fuskanta ba.
Joseph Kabila dai bai fito bainar jama'a ba tun bayan dawowarsa Goma ba. Amma 'yan tawayen M23 sun yi maraba da sanatan na dindindin da a kwanakin baya majalisar dattawan Kwango ta cire masa rigar kariya.