SiyasaAfirka
Kwango da M23 sun rattaba hannu kan yarjejeniyar sulhu
July 19, 2025Talla
Minista a ma'aikatar Harkokin Waje a Qatar Mohammed bin Abdulaziz bin Saleh Al Khulaifi, shi ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labaran Jamus dpa, inda ya ce sulhun zai bude sabon babin zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Karin bayani:Kwango da Ruwanda za su sanya hannu kan yarjejeniya
Ko a watan Maris 2025, shugaban Ruwanda Paul Kagame da takwaransa na Kwango Felix Tshisekedi sun yi ganawar ga-da-ga a birnin Doha na Qatar duk dai a kokarin shawo kan rikicin. Rikicin dai ya samo asali ne tun lokacin da mayakan M23 suka karbe iko da birnin Goma da ke gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da kuma mamaye lardunan Arewaci da kuma Kudancin Kivu.