Kwamitin Sulhu na MDD na zama kan harin Isra'ila a Iran
June 13, 2025Kwamitin Sulhu na MDD na taron gaggawa a wannan Juma'a bayan kazamin harin da Isra'ila ta kai wa Iran a wurare sama da 100 kamar yadda tawagar Guyana wacce ke jagorantar zaman majalisar a watan Juni ta sanar.
Wata majiyar diflomasiyya ta shaida wa kafanin dillacin labaran Faransa AFP cewa Iran ce ta bukaci kwamitin ya zauna, bukatar da ta samu goyon bayan Rasha da China.
Iran dai bayyana hare-haren na Isra'ila a matsayin 'ayyana mata yaki gadan-dagan' sannan ta kuma yin alkwarin mayar da martani mai zafi wanda zai sa Isra'ilar yin nadama.
A yayin wadannan hare-hare dai Isra'ila ta lalata wa Iran cibiyoyin nukiliya da dama tare ta halaka wasu manyan kwamandojin juyin juya hali da kuma masana kimiya.
Shugaban Amurka Donald Trump ya shawarci Iran da ta gaggauta amincewa da yarjejeniya kan shirinta na nukiliya tun kafin guri ya kure mata, yana mai gargadin cewa hare-haren za ta fuskanta a nan gaba za su kasance mafi muni.