Yemen: Kwale-kwale ya kife da 'yan Afirka
August 4, 2025Jirgin ruwan da ya kife a gabashin birnin Aden mai tashar jiragen ruwa a kasar Yemen, yana dauke da mutane 150 mafi akasari 'yan kasar Habasha. Jami'an tsaron gabar tekun sun gano gawarwaki 76, tare da ceto mutane 32. Wani jami'in tsaro ya ce an kai wasu daga cikin wadanda aka ceto zuwa birnin Aden kusa da Abyan. Babban jami'in hukumar kula da 'yan cirani a kasar Yemen Abdusattor Esoev ya shaidawa kamfanin dilancin labaran Faransa na AFP cewa: "hatsarin jirgin na daya daga cikin hadura mafiya muni na 'yan ci-ranin da suka nutse a gabar Tekun Yemen a bana."
Jirgin dai ya nufi lardin Abyan ne da ke kudancin Yemen, inda ake yawan samun kwale-kwale na safarar bakin haure 'yan Afirka. Duk da yakin basasar Yemen da ya talauta kasar tun shekarar 2014, ammaa ta kasance babbar hanyar safarar bakin haure ba bisa ka'ida ba, musamman daga Habasha da ke fama da rikicin kabilanci. Cardinal Pietro Parolin, sakataren harkokin waje na fadar ta Holy See, ya ce "Fafaroma ya yi matukar bakin ciki da asarar rayuka da aka yi."
Karin Bayani:
A kowace shekara, dubban mutane na kasada a hanyar da ake kira “Hanyar Gabas” daga Djibouti zuwa Yeman ta Tekun Bahar Maliya, domin zuwa Kasashen Gulf kamar Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa. Rahoton hukumar IOM ya ce akalla mutane 558 sun mutu a Tekun Bahar Maliya a 2024, wasu 462 sun mutu ne ta dalilin hadarin kwale-kwale. Hukumar IOM ta bayyana lamarin a matsayin"mai ratsa zuciya," inda ta jaddada bukatar gaggauta samar da hanya mara hadari don kare lafiyar bakin haure. Mutane 350 sun mutu a hanyar daga farkon 2025 zuwa watan Agusta na 2025 din.
Hatsarin da bakin haure ke fuskanta a hanya
A kan hanyarsu ta zuwa Tekun Fasha, bakin hauren na ratsa mashigin Bab al-Mandab, mashigar ruwa da ke bakin Tekun Bahar Maliya, wadda ita ce babbar hanyar kasuwanci ta kasa da kasa, da kuma yin kaura da safarar mutane. Da zarar sun shiga Yemen, kasa mafi talauci a yankin Larabawa. Bakin hauren dai, kan fuskanci barazana ga tsaron lafiyarsu.
Hukumar IOM ta ce dubun-dubatar bakin haure sun makale a kasar Yeman, kuma suna fuskantar cin-zarafi a lokacin tafiyarsu. A cikin watan Afrilu, sama da mutane 60 ne suka mutu a wani harin da Amurka ta kai kan wata cibiyar tsare bakin haure a kasar, a cewar 'yan tawayen Huthi da ke rike da galibin kasar. Masarautun Gulf masu arziki suna karbar bakuncin man'yan ma'aikatan kasashen waje daga Kudancin Asiya da Afirka.