Kwalara ta salwantar da rayuka a Sudan
August 14, 2025Talla
Kungiyar likitoci masu agaji ta Doctors Without Borders ta ce barkewar annobar na daga cikin tashin hankali mafi girma da al'ummar kasar ke fuskanta, tun bayan barkewar yaki a kasar tsakanin dakarun gwamnati da kuma rundunar kar-ta-kwana ta RSF.
Shugaban kungiyar likitocin a Sudan Tuna Turkmen, ya ce lamarin na neman gagarar kundila, kasancewar cutar na yaduwa cikin hanzari a kasashen Chadi da Sudan ta Kudu wadanda ke makwabtaka da Sudan.
Kungiyar ta doctors Without Boarders ta ce ta kula da marasa lafiya akalla 2,470 a wannan wata na Agusta daga cikin mutane dubu 99,700 da suka kamu da cutar ta kwalara.