Kungiyoyin agaji sun yi gargadi kan karuwar yunwa a Gaza
July 23, 2025Talla
Isra'ila dai na fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya kan mummunan halin da ake ciki na jin kai a yankin Falasdinu, inda sama da mutane miliyan biyu ke fuskantar karancin abinci da sauran muhimman abubuwa, bayan shafe watanni 21 ana rikici.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce sojojin Isra'ila sun kashe Falasdinawa sama da 1,000 a yayin da suke kokarin samun agajin abinci, tun bayan da Amurka da Isra'ila suka fara gudanar da ayyukan jin kai a Gaza a karshen watan Mayu, matakin da ya yi hannun riga da tsarin da MDD ke jagoranta.
Daga wayewar gari zuwa yanzu dai sojojin isra'ila sun kashe sama da Falasdinawa 20.