Kungiyoyin agaji na ketare za su fuskanci barazana a Rasha
July 13, 2012Majalisar dokokin Rasha ta amince da wani daftarin doka wanda ya baiyana kungiyoyi masu zaman kansu dake karbar tallafi daga kasashen waje a matsayin kungiyoyin leken asiri na kasashen ketare. Dokar wadda Amirka da kungiyar tarayyar turai suka yi Allah wadai da ita ta sami sahalewar 'yan majalisar dokoki 374 yayin da mutum uku kadai suka kada kuri'ar rashin amincewa sai kuma mutum guda wanda ya kauracewa kuri'ar. Sabawa dokar dai ka iya fuskantar hukuncin tara mai tsanani ko kuma dauri a gidan yari. Bugu da kari 'yan majalisar sun kuma zartar da wata dokar wadda ta baiyana batanci a rubuce ko da furuci a matsayin babban laifi da ka iya daukar hukuncin tara ta kudin Rasha rubles miliyan biyar kwatankwacin dala 152,000. Akwai tabbacin cewa majalisar dattijai ta kasar itama za ta amince da dokar kafin a mika ta ga shugaban kasa Vladimir Putin ya rattaba mata hannu. Wani dan majalisar dokoki na bangaren adawa Ilya Ponomarev yace dokar za ta kassara ayyukan sa kai da kungiyoyin farar hula masu zaman kansu suke gudanarwa.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Halima Balaraba Abbas