Red Cross ta fice daga Jamhuriyar Nijar
June 6, 2025Kungiyar ba da agaji ta kasa da kasa ta Red Cross ta bayyana rufe ofisoshinta na Jamhuriyar Nijar tare da ficewar ma'aikata 'yan kasashen ketere daga kasar. Haka na zuwa watanni hudu bayan hukumomin kasar ta Jamhuriyar Nijar sun bukaci kungiyar ta fice daga kasar da ke yankin yammacin Afirka.
Karin Bayani: Janar Tiani ya sake zargin Benin da Fransa da daukar nauyin 'yan ta'adda
Gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar karkashin Janar Abdourahamane Tchiani ta zargi kungiyar Red Cross da ganawa da 'yan tawaye, abin da ya fusata hukumomin daukan matakin korar kungiyar daga kasar.
Tuni kungiyar ta Red Cross ta musanta duk zargin da gwamnatin ta yi mata. Yanzu haka kungiyar tana taimakon kimanin mutane milyan biyu kan harkokin agaji. Shekaru biyu da suka gabata sojoji suka kifar da gwamnatin farar hula a kasar ta Jamhuriyar Nijar.