Hamas ta yi barazanar halaka 'yan Isra'ila da ke a hannunta
March 8, 2025Talla
Kungiyar Hamas ta yi barazanar halaka 'yan Isra'ila da take rike da su, muddin dai fada ya ci gaba a Zirin Gaza.
Hukumar leken asiri ta kasar Isra'ila ta ce Hamas na rike da 'yan kasar 24 da ma wasu gawarwakin mutum 35 da wasu kungiyoyin suka yi garkuwa da su a Gazar.
Amurka ta ce ta tattauna da Hamas a kan abin da ya shafi sakin wasu 'ya'yanta da su ma ke hannun kungiyar.
Ya zuwa yanzu dai Amurkar ta kasance cikin tattaunawa da Hamas din ne, ta masu shiga tsakani daga kasashen Isra'ila da Qatar da kuma Masar.
'Yan Isra'ila 33 ne dai kungiyar Hamas ta sako, a madadin Falasdinawa dubu biyu da Isra'ila ta tsare, bayan yarjejeniyar da aka cimma cikin watan Janairu.