Hamas ta amince da sabon daftarin tsagaita wuta a Gaza
August 18, 2025Kungiyar Hamas ta amince da sabon daftarin yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza wanda masu shiga tsakani Masar da Qatar suka gabatar mata, kamar yadda wani jigo a kungiyar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a Litinin din nan.
Karin bayani: Gaza: An gabatar wa Hamas sabon daftarin yarjejeniyar tsagaiata wuta
Jigon na Hamas da ya bukaci a sakaya sunansa, ya tabbatar da cewa bayan tuntubar juna, kungiyar da sauran kungiyoyi na yankin Falasdinu sun amince da sabon daftarin yarjejeniyar tsagaita wutar ba tare da neman a yi masa wata kwaskwarinma ba.
Sabon daftarin yarjejeniyar na kunshe da shawarwarin da Amurka ta gabatar da suka shata tsagaita wuta na tsawon kwanaki 60 da kuma sakin ragowar 'yan Isra'ila da Hamas ta yi garkuwa da su a lokacin harin ranar bakwai ga watan Oktoba wanda ya haddasa yakin Gaza.
Karin bayani: Mai zai faru bayan Isra'ila ta mamaye Gaza?
A yanzu kallo ya koma kan Isra'ila da ke shirin kaddamar da mamayar dan karamin yankin na Falasdinu domin kwace iko da birnin Gaza, duk kuwa da gargadin da wasu kasashe da kungiyoyin duniya ke yi mata.