EU za ta kara haraji ga manyan kamfanonin fasahar Amurka
April 11, 2025A wata tattuanawa da ta yi da jaridar Financial Times shugabar hukumar gudanarwar kungiyar EU Ursula von der Leyen ta ce a wannan yakin harajin na Shugaba Donald Trump, Amurka da Turai sun amince da dage karin harajin har zuwa wani lokaci don bada damar hawa teburin tattaunawa.
Amma Brussels ta ce a shirye take idan tataunawar diplomasiyyar ta gaza warware wannan takaddamar kasuwanci da gwamnatin Trump ta haifar za su dauki mataki a kan wadannan mayan kamfanonin.
Shugaban Amurka dai na ci gaba da fito na fito da kasashen duniya a kan harajin kasuwanci da ya kira hanya daya tillo donkawar da kwarar da ake yi wa kasarsa a fannin kasuwanci, inda kasar China ke a sahun gaba na karin harajin na Trump da kaso 145 yayin da a nasu bangaren mahukuntan Beijing tuni suka sanar da kara nasu harajin ga kayayyakin Amurka da kaso 125 cikin dari.
China wacce ta kira wannan matakin na Trump da cinzali ta bukaci hadin kan kasashen Turai domin yakar Trump.
Karin Bayani:Trump: Karin haraji na cike da kalubale