Kungiyar AES ta kulla yarjejeniyar kasuwanci da Maroko
April 29, 2025
Kungiyar AES da ta kunshi kasashen Burkina Faso Mali da Jamhuriyar Nijar, ta amince da kulla yarjejeniyar kasuwanci da kasar Moroko domin ratsawa ta tashoshin ruwan kogin Atlantic. Ministocin harkokin wajen kasashen uku da ke karkashin mulkin sojoji ne suka wakilci AES, wajen ganawa da sarkin Morocco Mohammed na 6 a birnin Rabat, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta tabbatar.
Karin bayani:Ghana ta fara wani sabon yunkuri na dawo da AES cikin ECOWAS
Maroko wadda ta yi fice a cikin harkokin noma da zuba jari da cinikayya, ta yi maraba da kasashen AES a cikin watan Nuwamban shekarar 2023, bayan da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta kakaba musu takunkumi sanadiyyar juyin mulkin sojoji.
Karin bayani:Aljeriya ta yi martani a kan kasashen AES
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da alaka ta yi tsami tsakanin Maroko da makwabciyarta Algeria har suka yanke hulda, sanadiyyar goyon bayan da Algeria ke bai wa 'yan Polisario da ke ikirarin cin gashin kai a yammacin Sahara.