Kotun Najeriya ta ce a bai wa mata kasonsu
April 7, 2022Murna ce dai ta baki har kunne ga matan Najeriyar da abin da suka gaza samu a majalisar dokokin kasar, a yanzu hakarsu ta cimma ruwa ta bin matakin shari’a domin kuwa bayan kwashe kwanaki suna fafutuka da ma zanga-zangar lumana a Abuja da wasu biranen kasar, a yanzu kotun tarayya inda mai shari’a Donatus Okorowa ya amince cewa lallai ana nuna wa matan Najeriyar bambanci a fannin mukamai, kuma nan take suka barke da murna.
Suwaiba Muhammad Dan Kabo, ita ce daraktar kula da shirye-shirye a kungiyar Actionaid mai kula da harkokin mata da ci gaban al‘umma a Najeriyar.
Tun shekarar 1995 bayan taron mata da aka yi a birnin Beijing na kasar China ne dai matan Najeriyar ke wannan fafutika cike da fuskantar tirjiya da cikas. Ta kai su ga barazanar amfani da kuri’arsu a zaben shekara mai zuwa don cimma burinsu, saboda watsi da kudurori biyar da majalisa ta yi. To sai dai ga Dorothy Nuhu Aken’ova, ta bayyana wannan a matsayin babbar nasara ga tafiyar matan.
Kungiyoyin mata ne dai suka tunkari kotu a Abuja a kan abin da suke ganin take masu hakki ne da nuna masu bambanci wajen samun mukamai a kasar da mata ne kan gaba wajen fitowa su yi zabe. Mufiliat Fujabi, ita ce shugabar asusun kula da harkokin mata a Najeriya.
Ta ce babu shakka wannan gagarumar nasara ce ba kawai a kansu ba har ma da sauran al’umma da za ta biyo bayan su, domin duk abubuwan da suka nema na a sanya mata a cikin harokin mulki kotu ta yi mana, wannan abu ne da za yi tasiri sosai.
Abin jira a gani shi ne aiwatar da wannan hukunci ga gwamnatin Najeriya wacce yanzu haka take fuskantar koke a fannin aiwatar da kashi biyar na ayyuka ga mutane masu bukata ta musamman watau naksassu ke nan na cikin kasar.