Kotun mulkin Koriya ta Kudu za ta fadi makomar shugaba Yeol
April 1, 2025Kotun tsarin mulkin Koriya ta Kudu ta tsayar da ranar Juma'a mai zuwa 4 ga watan Afirilu, domin zartar da hukuncin da aka dade ana jira kan makomar shugaba Yoon Suk Yeol da majalisar dokokin kasar ta tsige, bisa samunsa da laifin ayyana dokar ta-baci ta soja, wadda ta jefa kasar cikin rudani.
Karin bayani:Ana shari'ar karshe ta makomar tsige Yoon Suk Yeol
A ranar 3 ga watan Disamban bara Mr Yeol ya ayyana dokar soja ya kuma aika dakarun sojin zuwa majalisar dokoki don kwace ikonta, inda rikita-rikitar siyasar ta janyo wa kasar fadawa cikin tabarbarewar tattalin arziki da rashin sanin makomar shugabancinta.
Karin bayani:An gaza kama shugaban Koriya ta Kudu da aka tsige
Kafin tabbatar da tsige shugaba Yeol, sai alkali 6 daga cikin 8 sun amince da kudurin tukuna, daga nan sai batun shirya sabon zaben shugaban kasa a cikin kwanaki sittin.