SiyasaBrazil
Jair Bolsonaro zai gurfana a gaban kotu
August 15, 2025Talla
Ana tuhumar Bolsonaro da laifin yunkurin juyin mulki bayan zaben shugaban kasa na shekara ta 2022 da Luiz Inacio Lula da Silva ya lashe.
Tare da bakwai daga cikin abokan aikinsa, Jair Bolsonaro, mai shekaru 70, ana zarginsa da kokarin tabbatar da "dorewar ikonsa duk da kayen da ya sha daga Shugaba Lula .
A ranar takwas ga watan Janairu, shekara ta 2023, mako guda bayan rantsar da Lula, dubban magoya bayan Bolsonaro
suka mamaye hedikwatar cibiyoyi gwamnati a Brasilia, suna yin tir da magudin zabe tare da yin kira da cewar soja su tsoma bakinsu.