Kotun kolin Brazil ta umurci a tsare Bolsonaro a gidansa
August 5, 2025Kotun kolin Brazil ta ba da umurnin tsare tsohon shugaban kasar mai ra'ayin mazan jiya Jair Bolsonaro a gida, kafin ta yanke masa hukunci kan zargin kitsa juyin mulki.
Karin bayani: Brazil: Za a tuhumi Bolsonaro
Alkalin kotun Alexandre de Moraes ne ya ba da umurnin tsare Bolsonaro a gidansa da ke Brazilia tare da yin kashedin cewa idan ya yi wani yunkurin na karya wannan mataki zai fuskanci dauri na wucin gadi take-yanke.
Masu aiko da rahotanni sun ce an hango dandazon magoya bayan tsohon shugaban a gaban kotun kolin da ke Brazilia dauke da tutocin kasar a kafadunsu suna jaddada goyo baya a garesa.
Jair Bolsonaro mai shekaru 70 a duniya na iya fuskantar dauri na sama da shekaru 40 a gidan kaso, duk kuwa da goyon baya da yake samu daga shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya yi barazanar kara wa Brazil haraji a matsayin ramuwar gayya kan muzgunawa abokin dasawarsa.