Kotun kolin Amurka ta ba wa Trump damar korar baki
May 31, 2025Kotun kolin Amurka ta ba wa shugaban kasar Donald Trump damar aiwatar da manufarsa ta korar bakin haure a mataki na wucin gadi, inda zai iya soke takardun izinin zama a Amurka na bakin haure fiye da 530,000 'yan kasashen Venuzuela da Cuba da Nicaragua da kuma Haiti.
Karin bayani: Kotu ta yarda Trump ya kori yan Venezuela
A watan Maris da ya gabata ne dai sakataren tsaron cikin gida na Amurka ya soke shiri na musamman da Washington ta samar a karkashin gwamnatin Joe Biden da ta shude, wanda ya bai wa 'yan asalin wadannan kasashe hudu damar zama a Amurka na tsawon shekaru biyu saboda dalilai na yanayin kare hakkin dan Adam a kasashensu. Sai dai wani alkali da ke birnin Boston a arewa maso gabashin Amurka ya dakatar da wannan mataki a ranar 14 ga watan Afrilu, lamarin da ya kai gwamnatin Trump ga garzayawa kotun koli wadda ta dage wannan dakatarwar a jiya Juma'a kafin wata kotun daukaka kara ya yanke hukunci na dindindin a nan gaba.
Karin bayani: Donald Trump ya yi gargadin korar baki idan ya samu mulki
Tun dai a lokacin yakin neman zabensa Shugaba Trump ya sha alwashin korar bakin haure da ke zaune a Amurka ba bisa ka'ida ba, wadanda ya kira da sunan 'yan mamaya tare da zarginsu da zama gaggan masu aikata manyan laifuka.