Kotun Kamaru ta hana Maurice Kamto shiga zaben shugaban kasa
August 5, 2025Kotun tsarin mulkin Kamaru ta haramta wa jagoran adawar kasar Maurice Kamto tsayawa takarar shugaban kasa, a babban zabe mai zuwa na watan Oktoba, sakamakon rashin cika ka'idojin tsayawa takara.
Lauyansa Hippolyte Meli Tiakouang ne ya tabbatar wa manema labarai hukuncin kotun, bayan kammala zamanta na wannan Talata.
Mr Kamto mai shekaru 71, ya yi kaurin suna wajen sukar lamirin gwamnatin shugaba Paul Biya, kuma shi ne ya yi na biyu a zaben shugaban kasa na shekarar 2018, bayan tsayawa takara a jam'iyyar MRC.
A wannan karo kuma ya nemi tsayawa takarar a jam'iyyar MANIDEM, inda ya bayyana muradin tsayawar watanni biyar da suka gabata.
Karin bayani:An hana Tchiroma fita daga Kamaru zuwa Senegal
Yanzu haka dai shugaba Paul Biya mai shekaru 92, wanda ya shafe tsawon shekaru 43 yana mulkin Kamaru, zai sake neman wa'adi na takwas a kan karagar mulki ba tare da wata kwakkwarar adawa ba.