Kotun duniya ta yi watsi da karar Sudan kan rikicin Darfur
May 5, 2025Talla
Sudan dai ta zargi Dubai ne da ba da tallafin makamai ga mayakan sa kai na yankin Darfur, inda kotun da ta yi zama kan batun ta ce ta kori karar saboda ba ta da hurumi.
Cikin watan jiya ne Sudan ta nace a gaban kotun ta duniya cewar Hadaddiyar Daular Larabawa ta saba matsayin taron duniya kan batun kisan kiyashi inda ta bai wa mayakan yankin Darfur din makamai.
Daga nata bangare Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi amfani da damarta lokacin taron sanya hannu kan dokokin, tana mai nuna shakku kan batun tare da bayyana cewa kotun ba ta da iko kan zargin da Sudan ke yi mata dangane da rikicin na Darfur.