Kotun Chadi ta zargi wakilin RFI da hada baki da Rasha
April 10, 2025Wata kotun kasar Chadi ta ki amince wa da ba da belin wakilin kafar yada labaran Faransa ta RFI Olivier Monodji, tare da wasu 'yan jarida biyu, bayan zarginsu da hada baki da Rasha don yi wa kasar zagon kasa. Lauyansa Allahtaroum Amos ya ce suna da wa'adin kwanaki uku na daukaka kara, bayan kama shi a ranar 5 ga watan Maris din jiya da gwamnatin Chadi ta yi, bisa zarginsa da aiki da kamfanin tsaro na Wagner wajen musayar bayanan sirri, domin yi wa kasar makarkashiya da leken asiri.
Karin bayani:Nijar ta janye sojojinta daga rundunar yaki da Boko Haram
'Yan jaridar uku na fuskantar hukuncin daurin shekaru 20 zuwa 30 a kurkuku, sai kuma wani 'dan jarida guda daya Ahmat Ali Adji da shi ma ke amsa tambayoyin kotu.
Karin bayani:An kaddamar da asusun farfado da tafkin Chadi
Babban jami'in kungiyar kare hakkin 'yan jarida ta Reporters Without Borders a kasar Sadibou Marong, ya yi kira ga mahukuntan Chadi da su sakar wa 'yan jarida mara su gudanar da aikinsu cikin kwanciyar hankali da lumana ba tare da muzgunawa ba.