Kotun Brazil ta tuhumi tsohon shugaba kasa da juyin mulki
March 26, 2025Kotun kolin Brazil ta ba da umarnin tuhumar tsohon shugaban kasar Jair Bolsonaro da aikata laifin shirya juyin mulki, lokacin da ya yi yunkurin jirkita sakamakon zaben shugaban kasa na shekarar 2022 da ya sha kayi.
Karin bayani:Brazil ta haramta wa Bolsonaro halartar bikin rantsar da Trump
Dukkan alkalan kotun su biyar ra'ayinsu ya zo daya na zargin aikata laifin, kamar yadda ofishin babban mai gabatar da kara na kasar Paulo Gonet ya shigar da tuhuma, laifin da ka iya janyo wa tsohon shugaban daurin shekaru 12 a kurkuku.
Karin bayani:Shugaban Brazil ya nemi duniya ta magance sauyin yanayi
Paulo Gonet ya zargi Bolsonaro da hada baki da mukarrabansa, domin zarce wa a kan karagar shugabancin Brazil, duk kuwa da shan kayi a hannun Luiz Inácio Lula da Silva a shekarar 2022, inda kuma a ranar 8 ga watan Janairun 2023 magoya bayansa suka far wa majalisar dokokin kasar da kotun koli, har ma da fadar shugaban kasa, tare da lalata kadarorin gwamnati.