Kotun Bangladesh ta fara karbar shaida kan Sheikh Hasina
August 3, 2025Shaida na farko a shari'ar da ake yi wa hambararriyar firaministar Bangladesh Sheikh Hasina, ya gurfana gaban kotu ranar Lahadi, tare da gabatar da hujjoji bayan harbinsa da bindiga a fuska da jami'an tsaro suka yi bara, yayin zanga-zangar da ta yi sanadiyyar kawar da ita daga kan karagar mulkin kasar.
Mutumin mai suna Khokon Chandra Barman, na daya daga cikin shaidun da kotun za ta saurara kan tuhume-tuhume 11 da ake yi wa Sheikh Hasina, da ta jima da tserewa zuwa kasar Indiya, inda ta samu mafakar siyasa.
Karin bayani:MDD: Tsohuwar gwamnatin Bangladesh ta murkushe masu bore 1,400
Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, ya nuna cewa kimanin mutane 1,400 aka kashe a Bangladesh, daga watan Yulin 2024 zuwa Agusta, sanadiyyar arangama tsakanin jami'an tsaron kasar da masu zanga-zangar nuna kin jinin gwamnatin Sheikh Hasina.