Kotu za ta yi hukunci kan yar tseren mita 800 Caster Semenya
July 9, 2025Hukumomin kwallon kafa a baya dai sun haramta mata shiga wasannin Olympics da sauran wasannnin cin kofin duniya na gudun famfalaki, sakamakon zargin samunta da kwayoyin halittun maza, wanda ke kara mata kuzari a wajen tsaren mita 800.
Karin bayani: Wasanni: Damben boxing da wasan guje-guje da kwallon kafa
Semenya ta lashe kofin duniya har sau biyu kafin fuskantar yankar kauna daga kotu, duk da daukaka karar da ta yi. Hukuncin kotun na Turai zai bude sabon babi kan takaddamar da ake yi kan mata-maza da kuma mata masu kwayoyin halittun maza wajen shiga wasannin mata zalla.
Karin bayani: Labarin Wasanni 07.11.2022
Caster Semenya dai ta ki shan magungunan da zasu rage tasirin kwayoyin halittun maza a jikinta kamar yadda hukumomin Afrika ta Kudu suka bukaci hakan, wanda kuma ya kawo karshen shaharar da ta yi a duniya.